Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta saukaka ayyukan shigowar mutane da kayayyaki cikinta
2020-09-24 20:54:02        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mista Wang Wenbin, ya furta a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta kara kebe wasu hanyoyi, domin saukaka ayyukan shigowar mutane da kayayyakin cikin kasar, karkashin manufar tabbatar da shawo kan yaduwar cutar COVID-19.

A cewar kakakin, yanzu haka, kasar Sin ta samu nasarori sosai a fannin dakile cutar COVID-19, inda tattalin arzikinta ke samun farfadowa sosai, sauran ayyuka masu alaka da samar da kayayyaki, da kyautata zaman rayuwar jama'a su ma sun koma yanayin da ake bukata, ta yadda kasar ta zama babban tattalin arziki na farko a duniya da ya fara samun karuwa, tun bayan abkuwar annobar COVID-19. Kana wannan yanayi zai haifar da alfanu ga farfadowar tattalin arzikin duniya.

Ban da haka, jami'in ya ce kasar Sin na son yin kokari tare da kungiyar kasashen Turai EU, don kulla wata huldar abota a tsakaninsu, musamman ma a fannin kare muhalli. Inda bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu, a kokarin tinkarar sauyawar yanayin duniya, don neman farfado da tattalin arzikin duniya, tare da kare muhalli. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China