![]() |
|
2020-09-22 13:51:58 cri |
Ya zuwa ranar Jumma'a, kimanin kashi 90 bisa 100 na daliban makarantun firamare, da na sakandare, da jami'o'i a fadin kasar Sin wanda ya kai adadin dalibai miliyan 242 sun riga sun koma cikin makarantunsu, hakan ya sa a yanzu aikin koyarwa ya kankama a fadin kasar Sin, kakakin ma'aikatar ilmin kasar Xu Mei ta bayyana hakan a yau Talala.
Xu Mei, ta bayyana a taron manema labarai cewa, a yanzu haka sabbin dalibai suna dakon shiga kwalejoji, a yayin da ake cigaba da bin matakai mafi dacewa na sake bude makarantun kasar domin dakile yaduwar annobar COVID-19.
Xu ta ce, ayyukan koyarwa ya kankama a makarantun kasar Sin bayan daukar matakai mafiya dacewa, ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa tsarin ilmin kasar ya jure babban ibtila'in annobar.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China