Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin Sin ya karyata zargin da shugaban kasar Amurka ya yi wa kasar Sin
2020-09-23 19:43:49        cri
Dangane da kalaman shugaban Amurka Donald Trump, kan batun da ya shafi kasar Sin, a yayin taron muhawarar babban taron MDD, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mista Wang Wenbin, ya furta a yau Laraba cewa, bangaren Amurka ya tsara karairayi, da shafawa kasar Sin kashin kaji, don neman biyan bukatarsa a fannin siyasa, don haka kasar Sin ba ta amince da kalaman na Trump ba.

Kaza lika hakikanin abubuwan da suka faru sun shaida cewa, abin da ya fi haifar da barazana ga al'ummun duniya, shi ne yunkurin daukar mataki na kashin kai, da manufar kashin dankali.

Ban da wannan kuma, game da wani labarin da ya nuna cewa, majalisar wakilan kasar Amurka, ta zartas da kudurin haramta shigar da kayayyakin jihar Xinjiang ta kasar Sin cikin kasar Amurka, mista Wang ya ce kasar Sin, za ta dauki duk wani matakin da ya wajaba, don kare hakkin kamfanonin ta. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China