Kakakin rundunar Sin: Yunkurin neman 'yancin kan Taiwan ba zai yi nasara ba
A yau Alhamis, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana yayin wani taron manema labaru cewa, dalilin da ya sa rundunar PLA ta kasar Sin ta aiwatar da atisaye a tekun dake dab da yankin Taiwan na kasar Sin, shi ne mayar da martani ga yadda wasu kasashen waje, ke neman yin shisshigi kan batun Taiwan, da 'yan tsirarun mutane masu ra'ayin balle yankin Taiwan daga kasar Sin, da aikace-aikacensu. A cewar kakakin, yunkurin neman 'yancin kan Taiwan, sam ba zai yi nasara ba. (Bello Wang)
Labarai masu Nasaba