Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda wani dan siyasar Amurka ke neman bata tsarin da ya shafi hadin gwiwar kasashe daban daban
2020-09-24 19:54:41        cri
A baya bayan nan, shugaban kasar Amurka ya sake bayyana kwayar cutar COVID-19 a matsayin "kwayar cutar kasar Sin", a taron muhawarar babban taron MDD. Kana ya yi takamar cewa, kasar Amurka ta samu nasarori da yawa a yunkurin dakile cutar, ko da yake a daidai lokacin da yake wannan jawabi, yawan Amurkawa da suka rasa rayukansu sakamakon harbuwa da cutar ya zarce dubu 200.

Ban da wannan kuma, wannan dan siyasar Amurka ya yi amfani da dandalin MDD, inda ya kamata a yi kokarin neman samun hadin gwiwar kasashe daban daban, ya nuna ra'ayinsa na dora laifi ga sauran kasashe, da daukar matakai bisa radin kai. Lamarin da ya zama wulakanci ga kundin tsarin MDD, da wani ra'ayi na bai daya da ake ma girmamawa, na kasancewar bangarori daban daban masu fada a ji a duniyarmu.

A wannan lokaci da duniyarmu ke ci gaba da fuskantar barazanar bazuwar cutar COVID-19, ya kamata a dora muhimmanci kan batun hadin gwiwa a tsakanin kasashe daban daban, don neman daidaita al'amura. Amma wannan shugaba na wata kasar da ta fi karfin tattalin arziki a duniya, bai lura da yanayi mai wuya da ake ciki ba ko kadan. Maimakon haka, ya yi kokarin yada jita-jita da karairayi, da neman ta da rikici tsakanin kasashe daban daban, lamarin da ya saba wa al'adar aikin diplomasiyya, da kuma manufofi masu dacewa. Hakan ya kara nuna yadda kasar Amurka ke son daukar matakai na kashin kai, da nuna ra'ayi na fin karfi a duniya.

Sai dai shugabanni na kasashe daban daban, ba za su yarda da karairayi da shugaban kasar Amurka ya yi ba. Inda da yawa daga cikin su, ciki har da shugaban kasar Faransa da shugabar gwamnatin kasar Jamus, ke bayyana bukatarsu ta karfafa hadin gwiwar kasashe daban daban, yayin da suke yin jawabi a wajen taron na MDD. Wannan ya nuna cewa, gamayyar kasa da kasa ba su yarda da ra'ayi na kashin kai ba, sa'an nan suna neman sauraron ra'ayi na bangarori daban daban, don cimma wata matsaya mai dacewa. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China