Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Garkuwar da Siyasa ta yi da kimiyya" ne ya sa kasar Amurka fadawa cikin taskun gaza dakile cutar COVID-19
2020-09-15 13:46:50        cri

A lokacin da yawan mutanen Amurka wadanda suka harbu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai kusan miliyan 6.5, har ma wadanda suka mutu sakamakon cutar suka kai kusan dubu dari 2, a kwanan baya, mujallar "Time" ta kasar Amurka ta koka da cewa "Amurka ta yi rashin nasara".

A hannu guda kuma, kwanan baya, kafar watsa labaru ta CNN ta kuma yi amfani da wani rahoton da makarantar koyon ilmin kiwon lafiyar jama'a ta sashen Berkeley na jami'ar California ta fitar, cewa, mai yiyuwa ne hakikanin yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ninka sau 3, har zuwa sau 20 bisa na adadin da aka fitar yanzu a Amurka. Wannan rahoto ya goyi bayan wani sakamako da cibiyar dakile cututukan ta Amurka CDC ta fitar a karshen watan Yulin bana, wato yawan mutanen da suka harbu da cutar ya zarce abun da aka yi tsammani.

Yanzu ga wani rahoton da abokin aikinmu Sanusi Chen ya hada mana.


A matsayin kasa mafi karfi a duk fadin duniya, me ya sa ta shiga hali mai tsanani irin wannan wajen dakile annobar? Mr. Thomas Frieden, tsohon shugaban cibiyar dakile cututukan kasar Amurka, ya nuna ba tare da rufa-rufa ba, cewar dabarar dakile cutar da gwamnati mai ci ta dauka ta sha kaye, har ma ba ta sake daukar matakai masu dacewa kamar yadda ya kamata ba. A hakika dai, idan mun duba abubuwan da 'yan siyasan kasar Amurka suka yi bayan barkewar annobar, za mu iya ganin cewa, asalin dalilin da ya sa ta shiga cikin halin shi ne, daga farko dai, Garkuwar da Siyasa ta yi da kimiyya, wannan ya sa gwamnatin Amurka ba ta iya daukar matakai masu dacewa bisa ilmin kimiyya kamar yadda ya kamata ba, wanda hakan ya sa kasar ta shiga cikin mawuyacin hali.

Ko da yake a kullum wasu masana kiwon lafiya suna nuna cewa, samar da bayanai a fili a kan lokaci yana da matukar muhimmanci, amma a ganin gwamnatin Amurka mai ci, mai yiyuwa ne boye hakikanin halin da ake ciki, zai iya hana bazuwar annobar. A kwanan baya, Bob Woodward, dan jaridar "Washington Post" ya fitar da wasu muryoyin da ya dauka, inda ya tona asiri cewa, a watan Faburairun bana, wato kafin wasu makwanni da tabbatar da farkon mutumin da ya mutu sakamakon kamuwa da annobar COVID-19, shugaban kasar Amurka ya riga ya san cewa, wannan annoba za ta iya bazuwa cikin sauri, har ma za ta iya sanya wadanda suka kamu da ita su mutu. Amma ba zato ba tsammani, a kullum yana cewa, "wata cutar numfashi ta mura kawai", har ma ya ce, "cutar za ta yi farat ta bace kamar wani yanayi na al'ajabi." Bayan Bob Woodward ya tona wannan asiri, wanda a kasar Amurka da ma sauran kasashen duniya an yi mamakin jin hakan kwarai.

Mr. Holden Thorp, babban editan mujallar "Nature", wato mujallar kimiyya mafi fada a ji, ya yi fushi ya zargin cewa, a matsayin shugaban kasar Amurka, ya yi karya kan batun kimiyya, irin wannan mummunan abun da ya yi, baya ga barazana ga lafiyar dan Adam, ya kuma haddasa dimbin mutuwar jama'ar Amurka. Ya ce "Mai yiwuwa ne, wannan ya zama abun kunya mafi tsanani a cikin manufofin kasar Amurka kan batutuwan kimiyya." Abin da ya sa aka fi nuna damuwa shi ne, yanzu, wasu 'yan siyasar Amurka, suna yunkurin cimma burinsu na kiyaye mutuncinsun siyasa, suna daukar matakin tilas na sake bude makarantu, domin suna cewa kowa zai iya samun karfin magance harbuwa da cutar da kan sa.

Lallai a idon 'yan siyasar Amurka, jama'a fararen hula, ciki har da dimbin yara dalibai su kasance kamar "beraye" da a kan yi amfani da su a dakin gwaji. Bugu da kari, sun yi kokarin dakile tasirin masanan kimiyya, har ma sun dauki matakan hana hukumomin kiwon lafiyar kasar fitar da ra'ayoyinsu, domin hana jama'a fararen hula, sanin hakikanin halin da ake ciki. Irin wadannan abubuwan da suka yi, sun bayyana yadda suke nuna adawa da hikimomin jama'a da kimiyya. A wani bangare kuma, su kan dauki matakan dora laifi ga wasu. Irin wadannan abubuwan da suka yi, su ne suka sa kasar Amurka shiga cikin hali mai tsanani sosai.

Yanzu karin mutane sun gane cewa, sabo da 'yan siyasar Amurka suna son cimma moriyar radin kansu, ya sa suka dauki matakan siyasa, na yi garkuwa da kimiyya, har ma sun sanya moriyar radin kansu a gaban rayukan jama'a, wanda hakan ya sa Amurkawa masu tarin yawa mutu kamar zubar ruwa maras amfani.

Matsalolin dake shafar Amurka ma sun kara tsananta, mutuncin kasar Amurka ya kara lalacewa a duniya. Abun tambaya dai a nan shi ne, shin ko irin wadannan 'yan siyasa wadanda suke sanya moriyar radin kansu a gaban moriyar kasa, da rayukan jama'a, za su iya "sake daga matsayin Amurka"? (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China