Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Idan za ka gina Ramin Mugunta ka Gina shi Gajere
2020-09-02 17:29:49        cri

A yayin da idon mahukunta Amurka ya rufe, har suke ta musgunawa kamfanonin kasar Sin dake kasar, ta hanyar hana su gudanar da harkokinsu na kasuwanci kamar yadda tsari da dokokin cinikayyar kasa da kasa suka tanada, a wasu lokutan ma suke cewa, wai wasu kamfanonin kasar Sin tamkar barazanar tsaro ne ga Amurkar, ba tare da gabatar da wasu kwararan shaidu da za su tabbatar da ikirarin nasu ba.

Na baya-bayan nan da rashin adalcin Amurka ya shafa, ita ce manhajar Tik Tok. Amma kamar yadda malam Bahaushe ke cewa, gaskiya ba ta buya, kuma idan za ka gina ramin mugunta, aka ce ka gina shi gajere, ko da wata rana za ka fada.

A yanzu tun ba a je ko'ina ba, Amurka ta fara fadawa ramin da ta haka da kanta, yayin da dalibai a wasu makarantu a kasar Amurka ke shirin fara sabon zangon karatu daga gida, saboda yadda cutar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban na kasar Amurka, ya sa kiyayya da ma harancin da Amurka ke sanyawa kamfanonin kasar Sin, yana neman dakushe burin dubban daliban makarantun sakandaren Amurka, na fara sabon zangon karatu ta hanyar amfani da nau'rar kwamfuta daga gida, saboda karancinsu ko jinkirin samar da wadannan na'urori da tilas sai daga kasar Sin za a kawo su kasar ta Amurka. Wai dan hakkin da ka raina, shi ke tsole maka idanu.

Kaikayi dai yana neman komawa kan mashekiya, domin a yanzu haka, irin wadannan makarantu, ba sa iya samarwa kowane dalibi kwamfutocin tafi da gidanka da suke bukata, don yin darasi daga gida. Duk da cewa, an fara sabon zangon karatu, amma dalibai da iyayen yara a Amurka na cikin matsala. Yanzu haka ma, makarantun gundumomi a kasar, suna bukatar iyayen yara, da su biya kudaden na'urorin da za a koyar da yaransu daga nesa a aljihunsu.

A lokacin da 'yan siyasar Amurka suke neman hana kamfanonin kasar Sin gudanar da harkokinsu na cinikayya a kasar, wasu 'yan kasuwa da masu fashin baki da suka san abin ka iya biyo baya, sun gargadi jami'an gwamnatin Amurka, da su yi watsi da wannan gurguwar shawara, domin ba zai haifarwa kasar da mai ido ba, amma abin ka da wanda ya yi nisa, aka ce ba ya jin kira. Yanzu dai sun fara ganin mummuman sakamakon da da a baya masana suka yi hasashen ka iya faruwa. Wanda bai ji gari ba, zai ji huhu.

Masana harkar Ilimi dai, sun nuna damuwa cewa, karancin kwamfutocin tafi da gidanka, na iya fadada gibin kwazo tsakanin dalibai, matakin da zai iya haifar da rashin daidaito a tsarin zamantakewa. A don haka ne ma, suka yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta hanzarta magance wannan matsala tun kafin wankin hula ya kai su dare. Amma abin da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Yanzu ta ina Amurka za ta fara? Magance yaduwar COVID-19 dake ci gaba da halaka 'yan kasar, ko kuma mummunan halin da tattalin arzikin kasar ya shiga, baya ga wasu tarin matsaloli da suka kaiwa ga 'yan kasar da dama rasa ayyukan yi? Ga kuma boren da kullum ke karuwa na nuna bambancin launin fata da tirkatirkar siyasar kasar, a daidai lokacin da aka shiga yakin neman zaben shugabancin kasar na watan Nuwanba. Sanin kowa cewa, idan har wasu rukunin daliban kasar ta Amurka ba su samu irin wadannan kwamfutoci ba, tamkar sun rasa damarsu ce ta samun Ilimi kamar kowa. Matakin da ya saba kudirin MDD na 'yancin samun Ilimi mai inganci ga kowa ne yaro a duniya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China