Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin CDB na kasar Sin ya samar da dimbin rance don taimakawa shirin kawar da talauci
2020-09-20 16:40:09        cri
Bankin raya kasa na kasar Sin CDB, ya gabatar da wasu alkaluma a kwanan baya cewa, daga shekarar 2016 zuwa karshen watan Agustan da ya wuce, bankin ya riga ya samar da rancen kudi da ya kai RMB Yuan triliyan 1.5 (kwatankwacin dalar Amurka biliyan 222), don taimakawa shirin fitar da matalautan kasar daga kangin talauci, da raya wasu wuraren da ke fama da talauci a kasar Sin.

A cewar bankin na CDB, a 'yan shekarun baya bayan nan yana dora muhimmanci ga aikin kawar da talauci, kana ya yi kokarin hadin gwiwa da hukumomin kasar, don samar da karin tallafi ga yankunan dake da bukata.

Bankin CDB wani banki ne mai kula da ayyukan samar da bashi, da zuba jari, don taimakawa gudanar da wasu manyan tsare-tsaren raya tattalin arzikin kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China