Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Sin sun yi atisaye a kusa da mashigar yankin Taiwan
2020-09-18 15:53:36        cri

Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya sanar a ranar Juma'a cewa, rundunar sojojin 'yantar da al'ummar kasar Sin, PLA, ta gudanar da atisayen soji a kusa da mashigar yankin Taiwan.

Ren Guoqiang, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya ce, daukar wannan mataki ya zama tilas bisa la'akari da halin da ake ciki a mashigar yankin Taiwan, domin tabbatar da ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasar.

Da yake jaddada kasantuwar yankin Taiwan a matsayin bangaren da ba za a taba balle shi daga babban yankin kasar Sin ba, Ren ya ce, batun dake shafar Taiwan wani al'amari ne na harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma ba za a taba lamintar tsoma bakin bangarorin kasashen ketare ba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China