Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Amurka za ta sauke nauyin dake wuyan ta game da martaba yarjejeniyar kwance damara
2020-09-11 20:24:08        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce kasar Sin na fatan Amurka za ta sauke nauyin dake wuyan ta, na martaba yarjejeniyoyin kasa da kasa na kayyade kera makamai.

Zhao ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na yau Juma'a. Yana mai cewa, bai kamata Amurka ta yi kafar ungulu ga yarjejeniyoyin ba, ko ta jefa tsarin samar da daidaito na duniya cikin hadari.

Wasu rahotanni sun bankado yadda wani dan jaridar Amurka, ya bayyana cikin wani littafi da ya rubuta cewa, shugaban Amurka Donald Trump, ya furce yadda kasar sa ke aikin kera sabbin makaman nukiliya a boye.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hakan, Zhao Lijian ya ce a matsayin ta na kasar da ta fi yawan mallakar makaman nukiliya masu zamani, Amurka ta karya kudurin da kasashen duniya suka cimmawa, ta kuma ki amincewa ta sauke nauyin ta na musamman, game da kwance damarar makaman nukiliya, a hannu guda kuma tana ingiza takarar hakan tsakanin manyan kasashen duniya.

Kaza lika jami'in ya ce, Amurka na yawan karya yarjeniyoyi da aka kulla da ita, yayin da take kara azamar bunkasa sarrafa nukiliya. Wanda hakan na gurgunta amincewa da martaba juna tsakanin kasa da kasa, tare da ingiza hadarin ma'amala da nukilya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China