Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin kasashen waje suna da imani kan kasuwannin kasar Sin
2020-09-16 15:56:17        cri
Wasu mutane na zargin wai kamfanonin kasashen waje suna janye jiki daga kasar Sin. Dangane da hakan, kakakin kwamiti mai kula da raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin Meng Wei, ta bayyana a yau Laraba cewa, hakika kamfanonin suna da imani kan ci gaba da zuba jari a kasar Sin.

A wajen wani taron manema labaru, Meng ta ce, a ranar 9 ga wata, kungiyar 'yan kasuwan kasar Amurka dake birnin Shanghai na kasar Sin, ta gabatar da wani rahoto, inda ta ce yawancin mambobin kungiyar suna sa ran ganin karuwar kasuwannin kasar Sin, kana kashi 78.6% daga cikin kamfanonin da suka halarci bincike sun ce ba za su janye jiki daga Sin ba.

Sa'an nan a ranar 10 ga wata, kungiyar 'yan kasuwan kasashen Turai dake kasar Sin ta gabatar da wani rahoto dake cewa, kashi 11% na kamfanonin Turai ne kawai ke da shirin sauya tsarinsu na zuba jari a kasar Sin.

Wadanna alkaluma, a cewar Madam Meng, sun nuna cewa, kamfanonin kasashen waje suna da imani sosai kan ci gaba da zuba jari ga kasar ta Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China