Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu cutar COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 1.39, mutane 33,626 sun mutu
2020-09-20 15:58:08        cri
Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a Afrika ya kai 1,390,560 ya zuwa ranar Asabar, cibiyar yaki da cutuka masu yaduwa ta Africa CDC ce ta bayyana.

Hukumar dakile cutuka ta nahiyar ta bayyana cikin sanarwar da ta fitar cewa, yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar annobar COVID-19 a Afrika ya kai 33,626 ya zuwa ranar Asabar.

Sai dai hukumar ta ce, jimillar mutanen da suka warke daga annobar a duk fadin nahiyar ya kai 1,140,980 ya zuwa yanzu.

Da take karin gaske game da tasirin annobar ta COVID-19 a kasashen Afrika, Africa CDC ta ce, kasashen da annobar ta fi shafa a nahiyar sun hada da Afrika ta kudu, Masar, Morocco, Habasha da Najeriya.

A cikin makon da ya gabata, kasar Morocco ta samu adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da annobar ta COVID-19, inda aka samu sabbin mutane 14,603 da suka kamu da cutar, sai Afrika ta kudu da Habasha da suke bi mata baya da sabbin adadin masu kamuwa da cutar 11,013 da kuma 4,742. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China