Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Africa CDC ta ce kasashen Afrika 32 sun samu masu kamuwa da COVID-19 kasa da 5,000
2020-08-25 10:43:24        cri

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Africa CDC, ta sanar a ranar Litinin cewa, kasashen Afrika 32 sun samu rahoton masu kamuwa da cutar COVID-19 kasa da 5,000 yayin da ake samun karuwar sabbin masu kamuwa da cutar a wasu kasashen Afrika 'yan kalilan.

A sanarwa da Afrika CDC ta fitar ranar Litinin ya nuna cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 1,187,937, kana wadanda cutar ta kashe ya kai 27,779 ya zuwa ranar Litinin, sai dai a wasu kasahen Afrika 8 an samu adadin wadanda suka kamu da cutar tsakanin 5,000 zuwa 10,000.

Africa CDC ta ce kasashen Afrika uku da suka hada da Masar, Najeriya da Morocco, suna da jimillar adadin masu dauke da cutar COVID-19 kama daga 50,001 zuwa 100,000.

Kasar Afrika ta kudu ce kadai ta fi yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 da ya zarce 100,000 kawo yanzu, a yanzu haka an tabbatar da mutane 609,773 sun kamu da cutar a kasar. Sannan kuma kasar ce ta fi yawan mutanen da cutar ta kashe, wato mutane 13,059 sun mutu a sanadiyyar annobar ta COVID-19 a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China