Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi gwajin cutar COVID-19 sama da miliyan 12 a kasashen Afrika
2020-09-14 10:06:22        cri
Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce, kasashen Afrika sun gudanar da aikin gwajin cutar COVID-19 sama da miliyan 12.

Ya zuwa ranar Lahadi, an gudanar da gwajin cutar COVID-19 sama da miliyan 12 a fadin nahiyar Afrika daga cikin adadin an samu kashi 10 bisa 100 sun kamu da cutar.

A bisa ga alkaluma na baya-bayan nan daga Africa CDC, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai 1,346,658 ya zuwa ranar Lahadi. Adadin mutanen da cutar ta kashe kuwa ya karu zuwa 32,502 a yanzu haka.

A cewar kwararriyar hukumar lafiyar ta kungiyar AU, yawan mutanen da suka warke daga cutar COVID-19 ya zuwa yanzu ya kai 1,083,438.

Bugu da kari, daraktan hukumar Afrika CDC, John Nkengasong, ya bukaci kasashen Afrika su kara azama wajen kara yawan gwajin cutar ta COVID-19 domin a samu nasarar dakile bazuwar kwayar cutar a fadin nahiyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China