Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yaba kokarin nahiyar Afrika na yakar COVID-19
2020-08-26 10:43:02        cri
Jiya Talata, an gudanar da taron kwamitin kula da harkokin nahiyar Afrika na hukumar WHO karo na 70 ta kafar Intanet. Inda babban sakataren hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yaba matakan da Afrika ke dauka wajen yakar cutar COVID-19.

A cewarsa, dukkanin kasashen Afrika sun tsara shirin tinkarar annobar, kuma suna da karfin gano da kuma gudanar da bincike kan kwayar cutar. Ban da wannan kuma, ya jinjinawa kokarin da kasashen suke yi wajen tinkarar cutar.

Kazalika, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, hukumarsa za ta ci gaba da goyon bayan nahiyar don hana yaduwar cutar da kuma ceton rayukan mutane. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China