2020-08-08 16:46:21 cri |
Darakta janar na hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ba yadda za a yi a ci galaba a kan annobar COVID-19 idan kan kasashen duniya na rabe, inda ya ce yana fatan Amurka za ta sauya shawara kan matakinta na janyewa daga hukumar.
Tedros Adhanom Ghereyesus, ya bayyana yayin taron tsaro na Aspen da aka yi ta kafar bidiyo cewa, yanzu lokaci ne na hada hannu, kuma lokaci ne na mayar da hankali wajen yaki da kwayar cutar, a don haka yake fatan Amurka za ta sake shawara game da matsayarta.
Ya shaidawa mahalarta taron cewa, batun ba na kudi ba ne, abu mafi muhimmanci shi ne yadda duniya za ta hada kai wajen cin nasara a kan cutar mai hadari.
Ya ce idan akwai matsaloli dangane da tsarin WHO ko kuma MDD baki daya, kofarsu a bude take ga duk wani nazari ko tantancewa, yana mai cewa, za a iya gano gaskiyar lamari, kuma za a iya yin hakan ba tare da an janye daga hukumar ba. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China