Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Bai dace wata kasa ta yi zaton an kawo karshen COVID-19 ba
2020-09-01 10:01:25        cri

Babban dakartan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce hukumar sa na matukar fatan ganin yara sun koma makaranta, kana ma'aikata sun koma bakin ayyukan su, amma kuma a lokaci guda, a halin da ake ciki yanzu, ba wata kasa da za ta yi garajen bayyana kawo karshen cutar numfashi ta COVID-19 da ake fama da ita.

Mr. Tedros wanda ya bayyana hakan jiya Litinin, yayin taron manema labarai da ya gudana ta kafar bidiyo, ya ce idan har kasashen duniya sun damu da batun komawa bakin aiki, to kamata ya yi su kara azama wajen dakile hanyoyin yaduwar wannan annoba, tare da kare rayukan al'ummun su.

Babban jami'in na WHO ya ce "sake bude harkoki ba tare da shawo kan annobar ba, tarowa kai bala'i ne".

A cewar WHO, ya zuwa karshen jiya Litinin, bisa jimilla, adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 a dukkanin sassan duniya, ya kai mutane 25,118,689, ciki hadda mutane 844,312 da cutar ta hallaka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China