Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta kaddamar da dandalin koyarwa ta yanar gizo a arewa maso gabashin Somalia
2020-07-21 09:22:54        cri

Asusun yara na MDD UNICEF, da gwamnatin jihar Puntland dake arewa maso gabashin Somalia, sun kaddamar da wani dandalin koyar da yara ta kafar yanar gizo, wanda zai baiwa yara 'yan makaranta damar daukar darussa daga gida.

Ministan ma'aikatar ilimi mai zurfi na kasar Abdullahi Mohamed Hassan, ya ce dandalin zai samar da darussa masu nagarta, daidai da manhajar da aka tsara a hukumance, ta yadda yaran ba za su rasa damar samun ilimi sakamakon bullar cutar COVID-19 ba.

A karon farko sama da yara 11,000 ne za su shiga wannan shiri, wadanda sama da rabin su mata ne, inda za su samu darussa da aka nada sama da 600 domin yara 'yan firamare, kuma tuni aka dora irin wadannan darussa kan dandalin. Yaran na iya amfani da dandalin ta amfani da kwamfuta, ko kuma ta manhajar wayoyin hannu domin cin gajiyar dandalin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China