Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kaddamar da cibiyar bunkasa cinikayya tsakanin Sin da Afirka a Sin
2019-11-11 09:47:00        cri

Yanzu haka shirye shirye sun yi nisa, na ginin kashin farko na cibiyar bunkasa tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka a Gaoqiao dake birnin Changsha na lardin Hunan dake nan kasar Sin.

Ana fatan fara amfani da wannan cibiya ne a shekarar 2020 mai zuwa, inda za ta tattaro sassan hukumomi, da kungiyoyin kasa da kasa, da kamfanoni da kwararru daga sassan biyu.

Burin kafa wannan cibiya dai shi ne samar da damar fadada musayar hajoji tsakanin Sin da nahiyar Afirka, da samar da dama ta musayar kwarewa a sauran fannoni, kamar dai yadda ofishin lardin na Hunan, mai lura da harkokin ciniki ya tabbatar da hakan.

A cewar ofishin, lardin Hunan zai gina sakatariyar cibiyar tattalin arziki, da baje kolin hajoji tsakanin Sin da Afirka, baya ga samar da wasu sassan masu ruwa da tsaki da za su yi aiki cikin hadin gaiwa, domin fitar da wani sabon salon inganta cudanya tsakanin sassan biyu.

A shekarun baya bayan nan dai Sin da kasashen Afirka, na ci gaba da bunkasa hadin gwiwar su, karkashin dandali daban daban, ciki hadda na kasa da kasa na shige da ficen hajoji, da na hadin gwiwar Sin da Afirka dake taka muhimmiyar rawa wajen cimma nasarar da sassan biyu suka sanya gaba.

Sin ta kasance abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma cikin shekaru 10 da suka gabata. A shekarar 2018, darajar yawan cinikayyar sassan biyu ta kai dalar Amurka biliyan 204.2, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 20 bisa dari a shekara guda. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China