Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban majalissar dattijan Najeriya ya yi kira game da bunkasa dabarun habaka tattalin arzikin kasa
2020-09-17 09:57:10        cri
Shugaban majalissar dattijan Najeriya Ahmed Lawan, ya yi kira da a kara azama wajen bunkasa dabarun habaka tattalin arzikin kasarsa ta hanyar aiwatar da matakan inganta kwarewa, da bunkasa ingancin albarkatu.

Sanata Lawan ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yayin taro ta kafar bidiyo, na musayar ra'ayi game da inganta kwarewa, wanda kwamitin majalissar mai lura da bangaren, da kwamitin majalissar wakilan kasar mai lura da bunkasa albarkatu da sanya ido suka shirya.

Taron wanda shi ne irin sa na farko da aka gudanar, a matsayin damar baiwa al'ummar kasa ikon bayyana ra'ayoyi a fannin, na da nufin samar da zarafi na nazartar tasirin dokoki masu nasaba da batun, a gajere da dogon lokaci nan gaba.

Lawan ya ce kudurin dokoki masu nasaba da hakan, sun hada da na bunkasa cin gajiya daga albarkatun mai da iskar gas, wadanda aka tsara domin fadada takarar kasar, da bunkasa moriyarta a fannin.

Ya ce da tallafin hidimomi da ake samarwa a gida, da albarkatun dake fitowa daga masana'antun mai, ana fatan dokokin za su ba da gudummawar bunkasa sanin makamar aiki, tare da kiyaye bukatun kula da lafiya, da ingancin fannin.

Daga nan sai shugaban majalissar dattujan ya bayyana cewa, cutar numfashi ta COVID-19, ta tunawa 'yan Najeriya bukatar da ake da ita, game da dogaro da kai a fannin albarkatu, da karfafa sanin makamar aiki, da ma muhimmancin karfafa sassan cin gajiya a fannin sarrafa mai da iskar gas. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China