Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Najeriya sun karyata zargin da aka yi wa kasar Sin
2020-09-16 11:05:46        cri

A ranar 14 ga watan nan, jaridar "This Day" da ake wallafawa a Najeriya, ta wallafa wani bayani, dangane da hirar da aka yi da mukadashiyar shugabar cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya, Madam Ubi, da shugaban hadaddiyar kungiyar 'yan kasuwan jihar Lagos, mista Mabogunye, inda dukkansu suka karyata wani zargi da kungiyar Heritage Foudation ta kasar Amurka ta yi wa kasar Sin, cewa wai Sin ta sanya wasu na'urorin satan bayanai cikin gine-ginen da ta gina ma gwamnatocin kasashen Afirka.

A cewar Madam Ubi, wannan zargin da kungiyar Heritage Foudation ta yi ba shi da tushe ko kadan, don haka ya kamata kasashen Afirka sun yi watsi da wadannan jita-jita, da wasu makiyan kasar Sin ke kokarin yada su a duniya, tare da ci gaba da kokarin hadin gwiwa tare da Sin.

A cewarta, wasu kasashe masu sukuni sun fi sanin fasahar satar bayanai, misali wata kasar da ta mallaki kamfanin Google, da sauran shafukan sada zumunta da yawa, wadda ita ce kasar da ya kamata kasashen Afirka su kara mai da hankali kan ta, don magance tsunduma cikin tarko.

A nasa bangare, mista Mabogunye ya ce, bai kamata a gaskanta jita-jitar da ake yadawa game da kasar Sin ba. A cewarsa, kayayyakin more rayuwa da kamfanonin kasar Sin suka gina suna da inganci, wadanda suka taimakawa Najeriya a fannin raya harkar zirga-zirga, da kuma kasuwanci. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China