Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rotimi Amaechi ya bayyana kyakkyawan fata game da jami'ar da kamfanin CCECC ke ginawa a Najeriya
2020-09-04 10:04:07        cri
Ministan ma'aikatar sufurin tarayyar Najeriya Rotimi Amaechi, ya bayyana kyakkyawan fata game da makomar jami'ar harkokin sufuri, wadda kamfanin CCECC na Sin ke ginawa a garin Daura, na jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya.

An tsara samar da jami'ar sufurin ne domin bunkasa fasahohin da suka shafi sufuri, da musayar sabbin fasahohi da suka shafi fannin tsakanin Sin da Najeriya.

Cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafi, Mr. Ameachi ya ce jami'ar za ta samar da damar sada Najeriya da fasahohin inganta layukan dogo, tare da horas da 'yan kasar dabarun sanin makamar aiki, a bangaren kirar jiragen kasa da kuma gyaran su.

A watan Disambar bara ne dai kamfanin CCECC ya fara ginin wannan jami'a, a wani bangare na ba da gudummawar sa, ga harkokin kyautata rayuwar jama'a.

Yayin bikin kaddamar da ginin jami'ar, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce jami'ar za ta zama zakaran gwajin dafi, a fannin samar da kwarewar aiki, da kwararru a fannin gudanarwa, tare da bude kofofin kirkire kirkire a fannin sufuri, da kuma samar da karin guraben ayyukan yi ga 'yan kasar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China