Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 8 sun mutu a wani kwale kwale da ya kife a arewa maso yammacin Najeriya
2020-09-02 11:13:43        cri
Jami'ai sun tabbatar da mutuwar mutane takwas bayan da wani kwale kwale ya kife a jihar Kebbi dake shiyyar arewa maso yammacin Najeriya.

Sani Dododo, shugaban hukumar agajin gaggawa na jjhar Kebbi, ya fadawa 'yan jaridu cewa, mata biyu kadai aka ceto da ransu daga cikin fasinjojin. Mutane goma ne, da kuma matukin kwale kwalen suke cikinsa a lokacin da lamarin ya auku.

Sai dai kuma, jami'in yace, gawarwaki hudu ne aka gano kawo yanzu, ya kara da cewa, ana cigaba da gudanar da bincike domin nemo ragowar gawarwakin mutanen hudu.

Jami'an 'yan sandan yankin sun tabbatar cewa suna cigaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin kifewar kwale kwalen. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China