Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka da suka aiwatar da dabarun bunkasuwa ne kadai za su yi saurin fita daga tasirin COVID-19 a cewar wani masani
2020-09-16 10:53:56        cri
Wani masani a fannin shawo kan kalubale da hadurran tattalin arziki, kuma daraktan fannin, a cibiyar nazarin hadurra da ba da shawarwari ta kasa da kasa Mr. Barnaby Fletcher, ya ce kasashen Afirka da suka aiwatar da dabarun bunkasuwa ne kadai za su yi saurin tsira, daga tasirin COVID-19.

Mr. Fletcher ya bayyana hakan ne, yayin kaddamar da alkaluman tasirin matakan dakile hadurran tattalin arziki na Afirka na shekarar 2020, alkaluman dake nuna sakamakon bincike, game da tasiri mai tsayi da cutar numfashi ta COVID-19 ka iya yi ga nahiyar Afirka.

Masanin ya yi kira ga kasashen nahiyar, da su fadada harkokin raya tattalin arzikin su, domin rage radadin matsalar da ake fuskanta. Ya ce akwai yuwawar nahiyar Afirka ta fuskanci komadar tattalin arziki irinta ta farko cikin shekaru 25, yayin da kuma sassa masu zaman kan su ke kasancewa jigon farfadowar nahiyar.

A nasa tsokaci game da hakan, shugaban wata cibiyar nazarin tattalin arziki ta "NKC African Economics" Mr. Jacques Nel, kwazon da daidaikun kasashe za su yi ne zai tabbatar da nasarar su, ta farfadowa daga tasirin wannan cuta.

Mr. Jacques Nel, ya ce ga misali, ya zama wajibi ga Afirka ta kudu, ta magance karancin makamashi da take fuskanta. Kaza lika akwai bukatar kasar ta farfado da hada hadar kasuwanci, da karfafa gwiwar 'yan kasuwa ta hanyar inganta tsare tsare. Ya ce dole ne gwamnati ta bullo da dabarun farfadowa, don gamsar da sassa masu zaman kan su, game da tasirin wadannan dabaru. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China