Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manhajar TikTok ta kasar Sin ta gayyaci yan kasauwar Afirka shirin bayyana sanaoinsu
2020-09-10 10:40:45        cri

A jiya ne, manhajar raba gajerun hoton bidiyo ta kasar Sin, wato TikTok, ta gayyaci 'yan kasuwar kasashen Afirka, da su shiga shirin nan na tallafa sana'o'i da ya shahara a duniya.

Manajan shirye-shirye na tawagar TikTok dake Afirka, Boniswa Sidwaba, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka raba manema labarai cewa, sabbin kamfanoni dake Afirka da yankin gabas ta tsakiya, suna da dama har zuwa ranar 24 ga watan Satumba, don su gabatarwa manhajar TikTok da garejun hoton bidiyo na minti daya, da a ciki za su gamsar da tawagar kwararrun alakai ta duniya, ta hanyar amfani da na'urorin hada hotunan bidiyo masu sauki na manhajar.

Sidwaba ya bayyana cewa, shirin samar da tallafin, zai baiwa 'yan kasuwar dama shiga gasar zuba jari na kudin kasar Kenya Shilling miliyan 1.08, kwatankwacin dala dubu 10, da damar zama karkashin jagora na shekara guda daga gidauniyar Gritti, ta farko a duniya da ta shahara wajen faranta ran masu zuba jari.

A karshen shiri, mutane uku da suke yi nasara, za su yi tattaki zuwa Dubai, babban birnin hadaddiyar daular Larabawa, inda za a karrama su, ta hanyar gasar sauka kasa daga jirgin saman yawon shakatawa, a yayin da suke kammala gasar bi da bi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China