Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya taya Kim murnar cikar DPRK shekaru 72 da kafuwa
2020-09-09 13:54:37        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya takwaransa na kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un, murnar cika shekaru 72 da kafuwar kasar. A sakon da ya aika, shugaba Xi, ya ce yana dora muhimmanci matuka, kan raya alaka tsakanin Sin da Jamhuriyar al'ummar Koriya ta arewa (DPRK), kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Kim, don ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu gaba,don kara samun sabbin nasarori.

Xi ya yi nuni da cewa, a wannan lokaci mai muhimmanci, a madadin JKS, da gwamnati da al'ummar Sinawa, yana mika sakon taya murna da fatan alheri ga shugaba Kim, da jam'iyyar WPK, gwamnati gami da daukacin al'ummar koriya ta arewa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China