Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Ya dace Sin da Turai su nace kan manufofi hudu
2020-09-14 20:47:01        cri

A yammacin yau Litinin a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugabar karba karba ta kungiyar EU kuma shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Dorothea Merkel, da shugaban kungiyar kasashen Turai Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen ta kafar bidiyo, inda ya jaddada cewa, yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana kawowa kasashen duniya manyan sauye-sauye da ba a taba gani ba, daukacin bil Adam suna cikin wani yanayi a halin yanzu, don haka ya dace kasar Sin da kasashen Turai su tsaya tsayin daka domin ingiza huldar abokantaka dake tsakanin sassan biyu, haka kuma ya kamata su nace kan manufofi hudu wato zaman tare cikin lumana, da gudanar da hadin gwiwa ba tare da rufa rufa ba, da gudanar da harkokin kasa da kasa tsakanin bangarori daban daban, da kuma daidaita harkokin kasa da kasa ta hanyar yin tattaunawa.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China