Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya jaddada muhimmancin ci gaban kimiyya da fasaha wajen biyan bukatun kasa
2020-09-11 21:21:50        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ci gaba da bunkasa fannonin kimiyya da fasaha, don zurfafa biyan muhimman bukatun kasa.

Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne a birnin Beijing a Juma'ar nan, yayin wani taron karawa juna sani, wanda masana a fannin kimiyya da dama suka halarta.

Ya ce ya dace fannonin kimiyya da fasaha na Sin, su shiga matakan kasa da kasa, don fafatawa a gwagwarmayar tattalin arziki, su kuma kara haifar da kyakkyawan sakamako ga bukatun kasa, da rayuwar al'ummun ta, da fannin kiwon lafiyar su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China