Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da EU sun kulla yarjejeniya kan alkaluman da suka shafi muhalli
2020-09-14 21:33:16        cri

A yau ne, jagororin kasar Sin da na kungiyar tarayyar Turai, suka sanar da kulla yarjejeniya a hukumance kan alkaluman da suka shafi muhalli.

Jagororin sassan biyu dai, sun sanar da hakan ne, yayin ganawar da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kungiyar EU Charles Michel, da shugabar hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen suka yi, taron da ya gudana ta kafar bidiyo.

Shugabannin sun kuma yanke shawarar, kafa dandalin tattaunwar manyan jami'an sassan biyu, kan kare muhalli da matsalar sauyin yanayi, da dandalin tattaunawar manyan jami'an Sin da EU kan fasahohin zamani, da kulla hadin gwiwa a fannin fasahohi na zamani ba tare da gurbata muhalli ba.

Haka kuma, shugabannin Sin da EU, sun tabbatar da cewa, ya kamata a hanzarta sasanta yarjejeniyar zuba jari tsakanin Sin da EU, ta yadda za a cimma manufar sasantawa cikin wannan shekara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China