Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi EU ta dakatar da tsoma baki a harkokin Hong Kong
2020-07-02 16:19:10        cri

Kakakin kungiyar jakadun kasar Sin da ke kungiyar Tarayyar Turai wato EU ya musunta kalaman da EU ta yi, dangane da yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin, tare da jaddada cewa, kalaman ba su da tushe, a don haka, ya kamata ta dakatar da tsoma baki cikin harkokin Hong Kong.

A jiya ne kuma, babban wakilin EU mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro ya ba da wata sanarwa, inda ya ce, ba a tattauna batun kafa dokar tsaron kasa a Hong Kong ba, kila hakan ka iya illanta yadda Hong Kong take tafiyar da harkokinta da kanta, da aiwatar da dokokinta, da tafiyar da harkoki bisa doka. Ya kuma bukaci kasar Sin da ta tabbatar da 'yancin mazauna Hong Kong da hakkinsu.

Kakakin kungiyar jakadun kasar Sin da ke EU ya jaddada cewa, makasudin tsara da kuma aiwatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong shi ne dakatar da duk wasu abubuwan da za su haifar da illa ga tsaron kasa a Hong Kong, da tabbatar da cewa, yankin Hong Kong yana bin manufar "kasa daya amma tsarin mulki 2", a kokarin ci gaba da aiwatar da kuma kyautata manufar, a maimakon sauya ta.

Kakakin ya ci gaba da cewa, yayin da tsara shirin dokar, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya saurari ra'ayoyin sassa daban daban, musamman ma bangarori masu ruwa da tsaki a Hong Kong. Ya kuma shirya tarukan bita guda 12 a Hong Kong a kwanan baya. Haka kuma, mazauna yankin Hong Kong kusan miliyan 3 sun sa hannu domin goyon bayan kafa dokar tsaron kasa a yankin. Mutane fiye da miliyan 1 da dubu 500 sun rattaba hannu ta Intanet domin nuna adawa da tsoma baki da kasashen ketare ke yi a harkokin Hong Kong, lamarin da ya nuna burin al'ummar Hong Kong. A don haka, kalaman EU game da yankin na Hong Kong, ba su da tushe sam. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China