Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude cibiyar gwajin cutar COVID-19 da kamfanin Sin ya gina a Angola
2020-09-13 16:59:05        cri

Tawagar kwararrun kamfanin BGI na kasar Sin dake kasar Angola ta tabbatar da bude cibiyar gwajin cutar COVID-19 ta zamani ta Fire Eye a Luanda, babban birnin kasar Angola, an gina cibiyar ne bisa hadin gwiwa da kamfanin BGI China, wanda a yanzu haka an kammala aiki har ma an bude ta, cibiyar za ta taimaka matuka wajen inganta aikin gano masu dauke da cutar COVID-19.

Ministan lafiyar kasar Angola, Silvia Lutucuta, ya bayyana a lokacin bikin bude cibiyar gwaje gwajen a Luanda cewa, cibiyar ta Fire Eye za ta taimaka wajen cike gibin aikin gano kwayar cutar a kasar ta hanyar fasahohin zamani. Bayan fara amfani da cibiyar, a halin yanzu, adadin aikin gwaje gwajen cutar a kasar a ko wace rana ya kai 3,000, wanda hakan zai yi matukar baiwa Angola gudunmawa a yaki da cutar COVID-19. Kasar Angola ta bayyana matukar farin ciki da kuma godiya ga gwamnatin Sin da kamfanonin kasar ta Sin bisa taimakon da suke baiwa kasar a yaki da annobar.

Baya ga cibiyar gwaje gwajen ta Fire Eye ta Luanda, akwai wasu karin cibiyoyin gwaje gwaje na Fire Eye guda uku da ake ginawa a sassa daban daban na kasar Angola.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China