Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumar FAO za ta taimakawa Angola a fannin tattara bayanai game da noma da kiwon kifi
2020-08-17 11:19:56        cri

Hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD ko FAO, ta sha alwashin taimakawa kasar Angola da kwararrun masana na kasa da kasa, da na bankin duniya, wajen aiwatar da wani shiri da aka yiwa lakabi da RAPP, wanda zai ba da damar tattara bayanai game da fannin noma da kiwon kifi a kasar.

Da take tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, yayin kaddamar da gangamin shirin na RAPP a yankin Gangula na lardin Cuanza Sul a kasar ta Angola, wakiliyar FAO a kasar Gherda Barreto, ta ce aiwatar da shirin zai sanya Angola zama kasar farko a Afirka a bana, wadda za ta ci gajiyar tattara muhimman bayanai game da fannin noma.

Jami'ar ta ce shirin zai bunkasa fannoni 7 dake cikin muradun samar da ci gaba mai dorewa na MDD, wadanda suka hada da yaki da yunwa da fatara, da bunkasa noma mai dorewa, da cimma daidaiton jinsi, da tabbatar da wadatuwar abinci.

Barreto ta kara da cewa, shirin tattara bayanan zai samar da damar amfani da su wajen fadada tattalin arzikin kasar, da kyautata matsayin ta na takara a fannin cin gajiyar albarkatun noma na al'umma, tare da samar da karin guraben ayyukan yi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China