Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon Darektan CDC: Matakan Amurka na yaki da COVID-19 ba su yi nasara ba
2020-09-11 15:35:06        cri
Tsohon darektan cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta kasar Amurka Thomas Frieden, ya bayyana cewa, matakan da gwamnatin tarayyar Amurka ta dauka na yaki da cutar nunfashi ta COVID-19, ba su yi nasara ba.

Da yake Karin haske yayin wata zantawa da gidan talabijin na CNN, Frieden ya ce Amurka ce kurar baya a fannin matakan yaki da COVId-19 a duniya, ya ce, kasar ba ta da tabbas, ba ta damu da halin da jama'a ke ciki ba, ba ta damu da sanya kwallen tufa baki da hanci ba a lokacin da ya dace, ba ta kuma dauki batun annobar da gaske ba, a wasu wurare ma, ba a dauki matakan dakile cutar a kan lokaci ba.

Frienden ya kuma nuna damuwa cewa, kalaman da shugaba Trump yake yi bainar jama'a game da barkewar cutar, yana iya dakushe kokarin mutane na yi musu riga kafin cutar.

A dangane da kalamai da abubuwan da Trump din yake yi da gangan, don ya shirirantar da annobar kuwa, Frienden ya damu cewa, hakan na iya shafar kokarin da ake na yiwa jama'a riga kafin cutar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China