Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin Amurka na hana kamfanonin kasar Sin gudanar da ayyukansu ya haddasa karancin kwamfutoci a makarantu
2020-09-01 19:19:48        cri

A yayin da cutar numfashi ta COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a galibin jihar California ta kasar Amurka, hakan ya sa kimanin dalibai 8,000 dake karatu a gundumar Mojave Desert Morengo su fara zangon karatunsu daga gida. Sai dai kuma, yadda gwamnatin Amurka ke kara sanyawa kamfanonin kasar Sin haramcin gudanar da harkokinsu na cinikayya, ya haddasa jinkiri ko kuma jinkirin kai wasu kayayyakin karatu daga nesa da suke amfani da na'urorin kasar Sin zuwa kasar

A halin yanzu, makarantar dake gundumar ba ta iya samarwa kowane dalibi kayayyakin koyarwa daga nesa. Duk da cewa, an fara sabon zangon karatu, amma dalibai da iyayen yara a Amurka na cikin hali. Galibin makarantun gundumomi suna bukatar iyayen yara, da su kebe kudi daga aljihunsu su biya kudaden na'urorin da za a koyar da yaransu daga nesa. A yanayin da ake fama da matsin tattalin arziki, gurgucewar harkokin kasuwanci da karuwar rashin ayyukan yi, galibin iyaye a Amurka suna ji a jikinsu.

Wasu Amurkawa masu kula da harkar ilimi sun nuna damuwa cewa, karancin kwamfutocin tafi da gidanka, na iya fadada gibin kwazo tsakanin dalibai, matakin da zai iya haifar da rashin daidaito a tsarin zamantakewa. A don haka, sun yi kira ga gwamnatin Amurka, da ta magance wannan matsala, saboda idan har wasu daliban ba su samu kwamfutoci ba, tamkar sun rasa damar koyo ne. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China