Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump zai tura jam'ian tsaron tarayya zuwa Kenosha na Wischonsin don magance tashin hankali dake faruwa
2020-08-27 13:55:04        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar a jiya Laraba cewa, zai tura jami'an tsaron tarayyar kasar zuwa birnin Kenosha na jihar Wisconsin, don kwantar da kurar da ta tashi, bayan da wani dan sanda ya harbi wani matashin bakar fata mai suna Jacob Blake.

A ranar Lahadi ne dai, wani dan sanda ya harbi Blake mai shekaru 29 sau bakwai a bayansa, aka kuma nadi bidiyon abin da ya faru. Iyalan Blake dai sun bayyana cewa, yanzu haka daga kugunsa zuwa kasa, ya shanye.

Yau an shiga rana ta uku a boren da ake yi, don nuna rashin jin dadi, da harbin bakar fatan, boren da ya rikide zuwa tashin hankali da barnata dukiya. Bayanai na cewa, wani harbi da aka yi a daren ranar Talata, yayin wannan zanga-zanga, ya yi sanadin kisan mutane biyu kana uku sun jikkata. A jiya kuma 'yan sanda sun kama wani matashi bisa zargin kisan mutanen biyu.

Kisan Blake na zuwa ne, watanni uku bayan kisin George Floyd, Ba-Amurke bakar fata dan shekaru 46, wanda ya mutu bayan da wani jami'in dan sanda ya makure wuyansa na tsawon kimanin mituna 9, yayin da ake neman kama shi a Minniapolis na jihar Minnesota.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China