Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta sake zama kasuwar dake kan gaba wajen sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki a karshen bana
2020-09-08 09:59:10        cri

Wani sabon rahoto da cibiyar dake bincike kan harkokin da suka shafi motoci ta kasar Jamus (CAR) ta fitar jiya Litinin, ya nuna cewa, ya zuwa karshen wannan shekara, kasar Sin za ta kama hanyar sake zama babbar kasuwar sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki (EVs) a duniya.

Hasashen cibiyar na nuna cewa, kasuwar irin wadannan motoci a yankin Turai a watanni shida na farkon bana, ta dan tashi, amma rawar da Elon Musk ya taka, za ta taimaka wajen bunkasa kasuwar kasar Sin, wadda ake ganin za ta ci gaba da jan ragamar kasuwar sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki na wasu shekaru 50 masu zuwa.

A cewar cibiyar ta CAR, baki daya, a watanni shida na farkon bana, an sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki da baturan da ake caji kimanin 400,000 a Turai. Sai dai kuma, a kasar Sin, an sayar da irin wadannan motoci da ba su gaza 7,200 a makamancin wannan lokaci.

CAR ta ce, kamfanin Tesla ne ya fito da sunan kasar Sin a harkar motoci masu amfani da wutar lantarki. A cewar cibiyar CAR, a watanni shida na farkon bana, kamfanin Tesla Shanghai giga, ya sayar da irin wadannan motoci kusan 50,000 a cikin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China