Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An mika rukunin farko na motocin Tesla kirar kasar Sin
2019-12-31 11:01:20        cri
A jiya ne, aka mika rukunin farko na motoci masu amfani da wutar lantarki da kamfanin Tesla na Amurka dake Shanghai ya kera. An dai mika motocin guda uku ne ga ma'aikatan kamfanin dake birnin Shanghai na kasar Sin.

Jami'an kamfanin sun bayyana yayin bikin mika motocin cewa, a watan Janairu ne, ake saran za a fara mika motocin ga kwastomin kamfanin da suka yi oda.

A watan Yulin shekarar 2018 ne, kamfanin Tesla da gwamnatin birnin Shanghai suka sanya kan wata yarjejeniyar kafa reshen hada motoci na kamfanin. A watan Oktoban shekarar 2018 kuma, aka baiwa kamfanin filin da ya kai sikwaya mita 864,885 a yankin Lingang, babban yankin masana'antu na zamani dake kudu maso gabashin birnin, domin ya bude reshensa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China