Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fiye da rabin motocin da ake sayar dasu a kasar Sin masu tamburan kasar ne
2020-08-15 16:23:45        cri
Jiya Juma'a, a wajen taron dandalin motoci na kasar Sin na bana dake gudana a birnin Shanghai na kasar, Mista Fu Binfeng, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masu kula da aikin sarrafa motoci ta kasar Sin, ya ce fiye da rabin motocin da ake sayar da su a cikin gidan kasar Sin, su ne motoci masu tamburan kasar, kana a cikinsu motoci masu daukar fasinjoji sun kai kashi 40%.

Ya fara daga shekarar 2009, yawan motocin da ake sayar da su a cikin kasar Sin ya zama na farko a duniya har shekaru 11 a jere, inda darajar motocin ta kai kashi 1 cikin kashi 3 na daukacin motocin da ake sayar dasu a duniya. Zuwa karshen bana ana sa ran ganin samun motoci miliyan 270 dake gudu a cikin kasar. A cewar mista Fu, wannan yanayi na samun cikakkiyar bukatar sayen motoci, yasa kamfanonin motocin kasar masu tambura na kansu samun damar raya kansu.

A nashi bangare, Christoph Wolff, mamban kwamitin zartaswa na dandalin tattalin arziki na duniya, ya ce ko da yake, annobar COVID-19 ta raunata harkar sayar da motoci a duniya, amma a cikin kasar Sin, harkar ta samu farfadowa sosai, har ma ta fara karuwa a watan Mayun bana, lamarin da ya nuna wani yanayi na jajircewa da kasuwannin kasar ke da shi.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China