Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin kera motoci GAC na kasar Sin ya baiwa Najeriya gudummawar yaki da COVID-19
2020-04-23 15:10:16        cri

Rukunin kamfanin kera motoci na GAC dake birnin Guangzhou na kasar Sin, ya baiwa Najeriya gudummawar kimanin dala dubu 51, don taimakawa kasar wajen yaki da cutar COVID-19.

Shugabar kamfanin a Najeriya, Diana Chen ta bayyana a jiya cewa, kamfanin ya baiwa hukumomim lafiya na jihar Lagos, cibiyar kasuwancin kasar da ma sauran sassan kasar, gudummawar motar daukar marasa lafiya da abubuwan rufe baki da hanci guda dubu 50.

Chen ta bayyana cikin wata sanarwa da aka aikawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, kamfanin ya hada kai da wasu fitattun mutane, don taimakawa ma'aikatan lafiya dake aikin yaki da wannan annoba a kasar dake yammacin Afirka.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce, karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Lagos tare da hadin gwiwar kungiyar Sinawa mazauna ketare a Najeriya, suka baiwa gwamnatin jihar Lagos gudummawar kimanin dala dubu 91 da kayayyakin kiwon lafiya, don taimakawa jihar yaki da cutar COVID-19. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China