Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan 'yan sandan Afirka ta kudu: Hari kan 'yan sanda tamkar cin amanar kasa ne
2020-09-07 11:15:51        cri

Ministan kula da harkokin 'yan sanda na kasar Afirka ta kudu, Bheki Cele, ya bayyana cewa, duk wani hari kan jami'an 'yan sanda, daidai ya ke da cin amanar kasa. Ministan ya bayyana haka ne jiya Lahadi, yayin da kasar ke makokin mutuwar jami'an 'yan sandanta da aka kashe a bakin aiki.

Ya ce, "zan ci gaba da daga murya na fada cewa, duk wani hari kan jami'in dan sanda, tamkar hari ne kan ikon kasa, kuma ya kamata a dauke shi tamkar cin amanar kasa." Cele ya bayyana haka ne, yayin bikin tunawa da ranar aikin 'yan sanda na kasar na wannan shekara, wanda aka yi bikinta a ranar 6 ga watan Satumba. A yayin bikin na bana, Cele ya kuma tuna da jami'an 'yan sandan da suka kwanta dama yayin da suke bakin aiki. Ya ce a shekarar da ta gabata, jami'an 'yan sanda 40 ne suka mutu a yayin da suke bakin aiki.

Shi ma mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu David Mabuza, ya bi sahun 'yan kasar, wajen karrama jami'an 'yan sanda da suka rasa rayukansa yayin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya, da tsaro da 'yanci a kasa.

Mabuza ya ce, gwamnati za ta ci gaba da inganta aikin dan sanda, ta hanyar samar musu da kayan aiki da kwarewa, da abubuwan kwadaitar da aiki, ta yadda za su gudanar da wannan muhimmin aiki na bautawa kasa ga 'yan kasar.

A cewar Mabuza, hukumar 'yan sandar kasar, tana karfafa kwarewar aiki ga mambobinta, ta hanyar samar da horo da nufin rage hare-haren da ake kaiwa 'yan sanda.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China