Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka ta kudu ta ayyana sake bude karin makarantu duk da ci gaba da bazuwar cutar COVID-19 a kasar
2020-07-06 10:06:38        cri

Ministar ma'aikatar ilimin bai daya ta Afirka ta kudu Angie Motshekga, ta bayyana shirin mahukuntan kasar na kara fadada bude makarantu, duk kuwa da karin masu harbuwa da cutar COVID-19 da ake samu a kasar.

Cikin wata sanarwar da ministar ta fitar, ta ce tun daga ranar 6 ga watan Yulin nan, za a bude ajujuwa rukunin R, da na 6 da 11. Hakan kuwa na zuwa ne, bayan da a ranar 8 ga watan Yuni, aka ayyana bude ajujuwa na 7 da 12, a zangon farko na bude makarantun kasar.

Tun bayan daukar wannan mataki ne kuma, ake samun rahoton karuwar malamai da dalibai da suke harbuwa da cutar a sassan kasar. A cewar ministar, alkaluman hakan sun shaida cewa, kawo yanzu, malaman makaranta 2,740 sun harbu da COVID-19 a kasar, adadin da bai kai kaso 1 bisa dari na jimillar malaman kasar 440,000 ba.

Kaza lika bayan bude wasu daga ajujuwan makarantun kasar, an samu dalibai 1,260 da suka kamu da cutar, adadin da ya yi daidai da kaso 0.01 bisa dari, na jimillar daliban dake ajujuwa na 7 da 12. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China