Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Goyon bayan juna da samar da abubuwan bukata ne kadai zai tabbatar da nasarar yakin da ake yi da COVID-19
2020-07-24 15:05:11        cri

Ministan ma'aikatar cinikayya a Afirka ta kudu Ebrahim Patel, ya ce goyon bayan juna tsakanin dukkanin kasashen duniya, da samar da muhimman abubuwan bukata na lafiya ne kadai zai tabbatar da nasarar yakin da ake yi, da cutar numfashi ta COVID-19.

Mr Patel ya ce bullar annobar COVID-19, ya kara fito da muhimmancin aiki tare a matakai na kasa da kasa, da gina yanayi mai karko, da tabbatar da ana rarraba kayayyakin bukata yadda ya kamata.

Ministan na wannan tsokaci ne, yayin taron ministocin cinikayya karo na 10 na kasashe mambobin kungiyar BRICS. Ya kuma ce a wannan gaba da cutar COVID-19 ke kara kamari, akwai bukatar karfafa hadin gwiwar dukkanin sassa.

Bugu da kari a cewar Patel, COVID-19 ta koyawa Afirka darasi, cewa nahiyar ba za ta iya kare al'ummar ta yadda ya kamata ba, muddin za ta ci gaba da fitar da kayan sarrafawa, ta kuma rika shigo da kayan da aka sarrafa ciki hadda magunguna, da kayan kula da lafiya, da sauran muhimman hajoji. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China