Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban Afrika ta kudu zai yiwa kamfanin lantarkin kasar garambawul
2020-09-04 10:37:36        cri

Mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu, David Mabuza, ya lashi takobin yin garambawul a tsarin kamfanin samar da lantarki na kasar Eskom, domin tabbatar da samun ingantacciyar wutar lantarki mai dorewa a kasar.

Mabuza, ya fadawa taron majalisar dokokin kasar cewa, gwamnati ta gamsu da irin nasarorin da aka samu wajen yin sauye sauye a kamfanin lantarkin kasar Eskom karkashin sabon shugabansa, Andre de Ruyter.

Lamarin ya zo ne bayan shiga wani zagayen daukewar wutar lantarki a kasar, lamarin da ya jefa kasar cikin duhu.

Mabuza ya ce, gwamnatin ta yanke kudirin taimakawa hukumar Eskom domin aiwatar da cikakkun manufofinta don samun damar wadata kasar da isasshen makamashi.

Sai dai Mabuza bai amsa tambaya game da ko za a sayar da hannayen jarin kamfanin Eskom mallakin gwamnatin kasar ba, amma ya baiwa 'yan Afrika ta kudu kwarin gwiwa cewa za su kawo karshen matsalar makamashin kasar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China