Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin ya jaddada tsayawar kasar kan turbar raya kasa tare da kokarin kare zaman lafiya
2020-09-05 21:11:42        cri
A ranar Alhamis da ta gabata, shugaban kasar Sin ya halarci wani taron tunawa da cika shekaru 75 da jama'ar Sin suka samu nasara a yakin kin harin sojojin Japan, kana jama'ar duniya suka samu dakile tafarkin murdiya, inda ya jaddada muhimmancin gadon wani ruhi na kin hari da kare kai, don tabbatar da ci gaban al'ummar Sin. A cewar shugaban, domin cimma burin raya al'ummar Sin, dole ne a tabbatar da rikewa da mulki da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ke yi, da tsayawa kan tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin, da tunanin mayar da moriyar jama'a gaban kome, da kare wani ruhi na gwagwarmaya da abokan gaba, gami da tsayawa kan raya kasa ta hanyar lumana.

Ban da haka, shugaba Xi ya kara da cewa, Sinawa ba za su taba yarda wani ko wasu makiya su jirkita tarihin JKS ko wargaza yanayi da manufarta ba.

Haka kuma al'ummar Sinawa ba za su taba bari wani ko wasu makiya su lalata ko sauya tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin ba, kin amincewa ko bata manyan nasarorin da al'ummar Sinawa suka cimma wajen gina tsarin gurguzu. Sinawa ba za su taba yarda wani ko wasu makiya su yi kokarin hada gaba tsakanin JKS da al'ummar Sinawa ba. Al'ummar Sinawa ba za su taba amincewa da wani yunkuri da wani ko wasu makiya za su yi na tilastawa kasar Sin ra'ayinsu, ko sauya alkiblar ci gaban kasar ko hana kokarin Sinawa na inganta rayuwarsu ba.

Al'ummar Sinawa, ba za su taba yarda da wani yunkuri daga wani ko wasu makiya na hana 'yancin al'ummar Sinawa na yin rayuwa da samun bunkasuwa cikin lumana ba, da yin musaya da hadin gwiwa tsakanin Sinawa da sauran al'ummun sauran kasashe, ko gwagwarmayar neman zaman lafiya da ci gaban bil-Adam.

Ban da wannan kuma, don tabbatar da zaman lafiya a duniya, kasar Sin ta zama zaunanniyar mambar kwamitin sulhun MDD wadda ta tura mafi yawan sojoji masu kiyaye zaman lafiya zuwa wurare daban daban. Tun da kasar Sin ta fara tura wasu hafsoshi 'yan kallo a shekarar 1990, zuwa yanzu kasar ta riga ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da dubu 40, wadanda suka tafi wuraren da ake rikice-rikice don taimakawa jama'ar wuraren samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. Zuwa shekarar 2018, kasar Sin ta rubuta manufar "tsayawa kan turbar neman samun ci gaba ta hanyar lumana" cikin kundin tsarin mulkinta.

Sa'an nan a wannan karo, yayin taron da ya gudana a ranar Alhamis, shugaba Xi Jinping ya sake jaddada aniyar kasar Sin ta daukaka zaman lafiya, inda ya ce, jama'ar kasar Sin suna son zaman lafiya, kana za su yi kokari tare da jama'ar sauran kasashe, don neman tabbatar da makoma mai haske ga daukacin bil Adama. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China