Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Akwai bukatar aiwatar da matakai masu fa'ida game da sauyin yanayi don gane da farfadowa daga COVID-19
2020-09-04 11:06:39        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga gwamnatocin kasashen duniya, da su aiwatar da matakai masu ma'ana, game da shawo kan mummunan tasirin sauyin yanayi, karkashin dukkanin kudurorin su na farfadowa daga cutar COVID-19.

Antonio Guterres, ya yi wannan kira ne a jiya Alhamis, yayin da yake jawabi ga taron ministoci ta kafar bidiyo, game da dorewar manufofin farfadowa daga COVID-19, yana mai cewa, duniya na fuskantar manyan kalubale guda biyu, wato cutar COVID-19 da kuma sauyin yanayi.

Mr. Guterres, ya yi fatan ganin gwamnatoci, da bangarorin 'yan kasuwa, sun maida hankali ga wadannan fannoni, da nufin ganin amfani da makamashi mai tsafta, ya samar da karin guraben ayyukan yi, da iska mai tsafta, da ingancin kiwon lafiya, da kuma bunkasar tattalin arziki.

Kaza lika jami'in ya yi kira ga dukkanin kasashe, musamman ma mambobin kungiyar G20 ta kasashe masu karfin masana'antu, da su aiwatar da kudurin nan na kawar da fitar da iskar "carbon", nan da shekarar 2050.

A hannu guda kuma, yayin wannan taro, an kaddamar da wani dandalin yanar gizo, dake dauke da manufofin kyautata yanayi, da na kare muhalli, da kuma matakan farfadowa daga cutar COVID-19.

Ana sa ran dandalin zai ba da damar yin kwaskwarima ga manufofin taron COP26 na shekarar 2020, gabanin taron dake nazartar ci gaban da aka samu game da tunkarar matsalar sauyin yanayi, wanda ake sa ran gudanarwa a shekarar 2021 mai zuwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China