Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
COVID-19 ta yi tasiri ga alkaluman ci gaban kirkire kirkire na duniya na shekarar 2020 a cewar wani rahoto
2020-09-03 11:32:10        cri
Hukumar kare ikon mallakar fasahohi ta duniya WIPO, ta fitar da rahoton ta na bana, game da alkaluman ci gaban kirkire kirkire na duniya.

Rahoton wanda aka fitar a jiya Laraba, ya nuna yadda cutar numfashi ta COVID-19, take tasiri ga alkaluman ci gaban kirkire kirkire na duniya a shekarar ta bana. A cewar rahoton, wannan annoba na matsin lamba ga tsarin kirkire kirkire na duniya a dogon lokaci, don haka take fatan kasashen duniya za su karkatar da albarkatun su, wajen tabbatar da fannin kirkire kirkire ya ci gaba da samun kudaden gudanarwa yadda ya kamata.

A cewar babban daraktan jami'ar ilimin kasuwanci ta Turai Mr. Bruno Lanvin, ko shakka babu a halin da ake ciki, hadin gwiwar kasa da kasa, da fannin kirkire kirkire na fuskantar kalubale. Don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su karkata albarkatun su, wajen tabbatar da dorewar kudaden bukatu a fannin kirkire kirkire, ta yadda za a kaucewa kalubale da ka iya aukuwa ba zato ba tsammani.

A daya hannun kuma, masanin ya ce, yanayin bullar COVID-19 ya ba da gudummawa ga ci gaban wasu sassa na kirkire kirkire, da fannonin gargajiya, kamar fannonin kiwon lafiya, da na Ilimi, da yawon shakatawa da sayar da hajoji. Sauran sassan sun hada da hadin gwiwar binciken kimiyya, wanda shi ma ya kara karfafa.

Kaza lika gwamnatoci da dama, na aiki tukuru wajen samar da shirye shiryen gaggawa na rage radadin tasirin COVID-19, kamar batun dokokin kulle, da kuma shawo kan koma bayan tattalin arziki da ake fuskanta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China