Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres ya ayyana COVID-19 a matsayin mai sauya mahangar tsaro da zaman lafiyar duniya
2020-09-03 10:37:28        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya shaidawa shugabannin duniya cewa, annobar COVID-19 ta zama cuta da ta sauya mahangar duniya, game da bukatar wanzar da zaman lafiya da tsaro.

Antonio Guterres ya bayyana hakan ne, yayin wani taro ta kafar bidiyo da ya gudana jiya Laraba, game da kalubalen tsaro mai nasaba da bullar cutar COVID-19, da kuma dabarun gano bakin zaren ta, baya ga batun hade kan masu ruwa da tsaki a aikin, don cimma nasarar yakar barazanar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.

Babban jami'in MDDr ya kara da cewa, duniya ta shiga wani yanayi mai hadari, da sabon hali na rashin tabbas mai nasaba da bullar COVID-19, da tasirin ta ga tsaron kasa da kasa.

Tarukan baya bayan nan da MDD ke shiryawa ta kafar bidiyo, na samun halartar shugabannin Najeriya, da Philippines, da Kenya, da Bulgaria. Sauran mahalartan sun hada da firaministan kasar Canada, da Bulgaria, da Albania. Sai kuma manyan sakatarorin MDD da na hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa Interpol, da kuma mataimakin babban sakataren hukumar tsaro ta NATO. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China