Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF: Dokar kullen cutar COVID-19 ta shafi yara miliyan 463 a duniya
2020-08-28 09:59:05        cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF ya bada rahoton cewa daya bisa uku na yawan yara biliyan 1.5 a duniya dokar kulle makarantu sakamakon cutar COVID-19 ta shafi ilminsu inda basu samun damar halartar makarantu.

Babbar daraktar hukumar ta UNICEF Henrietta Fore, tace a kalla yara miliyan 463 wadanda aka rufe makarantunsu saboda cutar COVID-19, basu da wani tsarin koyar dasu a yankunan da suke. Adadin yaran da ilminsu ya gamu da cikas sakamakon rufe makarantun a watanni da dama ya kasance wani batun ilmi na gaggauta na kasa da kasa.

A cikin rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa, za a shafe gwamman shekaru ana jin radadin tasirin rufe makarantun a tsarin tattalin arziki da zaman rayuwar alumma.

Akwai bukatar samar da tsarin amfani da fasahohin zamani wanda za a yi amfani dasu a cikin gidajen domin karantar da yara 'yan makarantun reno, da firamare, da kananan sakandare, da kuma na babbar sakandare.

Rahoton ya bada shawarar amfani da kafofin talabijin, radiyo, da intanet don karantar da yaran a lokacin da ake cikin dokar kulle makarantun. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China