Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Cutar COVID-19 ta shafi lafiyar tunanin miliyoyin mutane
2020-08-28 10:18:50        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta shafi lafiyar tunanin miliyoyin mutane, ta fuskar shigarsu cikin damuwa da fargabar da cutar ta haifar musu, lamarin da ya haddasa tabarbarewar lafiyar tunaninsu.

Tedros ya fada a lokacin taron manema labarai a birnin Geneva cewa, ga mutane da dama, rashin samun damar yin cudanyar hada hadar yau da kullum wanda annobar ta haifar ya haddasa mummunar illa ga yanayin lafiyar tunaninsu.

Babban jami'in hukumar ta WHO ya kara da cewa, yanayin da mutane suka shiga na shafe dogon lokaci suna killace a wuri guda kamar gidaje, da cibiyoyin kula da masu tabin hankali ya kara tasirin girman matsalar, yace hatta su kansu kwararrun masana lafiyar tunanin dan adam kwayar cutar ta shafe su, kuma wasu daga cikin cibiyoyin kula da masu tabin hankali an mayar dasu zuwa wuraren jinyar masu fama da cutar COVID-19.

Jami'in ya ce, dama tuni an jima da yin rikon sakainar kashi ga batun kulawa da masu fama da tabin hankali a duniya tun gabanin bullar wannnan annoba, inda ake da yawan mutanen dake fama da matsalolin lafiyar tunani sama da biliyan daya a fadin duniya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China