Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Jamus ya gana da Wang Yi
2020-09-02 13:50:39        cri
A jiya ne, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a fadar sa, inda kuma suka yi shawarwari.

Shugaba Steinmeier, ya bukaci Wang Yi ya isar da gaisuwarsa zuwa shugaba Xi Jinping, tare da jaddada cewa, kasarsa na dora muhimmanci matuka ga dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, kana tana fatan kiyayewa, da zurfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Ya ce Jamus tana goyon bayan ka'idar Sin daya tak, da ra'ayin cudanyar bangarori daban daban a harkokin kasa da kasa, da rashin amincewa da ra'ayin janyewa daga tsarin duniya, kana ba ta son ganin duniya ta shiga halin nuna kiyayya ga juna ba.

A nasa bangaren, Wang Yi ya isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Steinmeier, yana mai cewa, duk da yanayin tinkarar cutar COVID-19 a dukkan duniya, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyara kasar Jamus da sauran kasashen Turai, wanda hakan ya shaida cewa, Sin ta dora muhimmanci ga dangantakar dake tsakanin ta da Jamus, da kuma Turai.

Har ila yau, Sin tana son yin kokari tare da Jamus, da sauran kasashen Turai, wajen shirya ajandar aikin da za a gudanar a mataki na gaba. Ya ce da farko, za a kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu wajen yaki da cutar COVID-19, ciki har da nazari da yin amfani da allurar rigakafin cutar, don kawo karshen ta ba tare da jinkiri ba. Na biyu kuma, ana fatan yin kira game da bin ra'ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da cin karensu babu babbaka, da tabbatar da ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma harkokin kasa da kasa cikin adalci. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China